Dalilin hana a kara wa tsohon shugaban EFCC, Lamorde girma zuwa DIG

0

PREMIUM TIMES ta gano cewa an cire sunan tsohon shugaban hukumar EFCC daga cikin sunayen manyan ‘yan sandan da aka kara wa girma zuwa DIG saboda wasu dalilai.

An ce an ki kara masa girma ne saboda akwai wasu manyan jami’an har su hudu da ke gaba da shi a wajen mukami da dadewa. Ana ganin idan aka kara masa girma zuwa DIG su kuma ba a kara musu ba, to abin zai janyo guna-guni da rabuwar kai.

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Lamorde shi ne babba daga cikin kwamishinonin ‘yan sanda 95 na kasar nan, ya na cikin wadanda aka rattaba cewa za a kara musu girma zuwa Babban Mataimakin Sufeto Janar.

Sai dai kuma yayin da aka fito da sunayen wadanda aka yi wa karin, sai ba a ga sunan Lamorde a ciki ba.

Majiya ba daya ba a cikin ‘yan sanda ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa akwai Mataimakan Sufeto Janar har hudu daga yankin Arewa maso Gabas inda Lamorde ya fito, wadanda sun fi shi mukami.

Ana ganin dalilin haka ne aka cire sunan sa, shi ya sa ba a kara masa girma yadda zai wuce su ba.

Amma wata majiya ta ce nan gaba za kara masa girma zuwa Mataimakin Sufeto Janar, wato AIG, maimakon Babban Mataimakin Sufeto Janar, wato DIG da aka nemi a cilla shi kwanan nan, kafin a canja tunani a cire sunan sa.

Share.

game da Author