Dalilin ganawar Buhari da sanatocin APC –Oshiomhole

0

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa baki daya, Adams Oshiomhole, ya bayyana dalilin ganawar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da sanatocin jam’iyyar APC.

Buhari ya gana da su ne da yammacin jiya Litinin a wata liyafar cin abincin dare a fadar sa.

Da ya ke jawabi bayan kammala taron, Oshiomhole ya bayyana ganawar ta yi matukar armashi.

Ya ce ya na da yakinin cewa ‘yan Najeriya za su kwarara wa sanatoci da mambobin majalisar tarayya na APC ruwan kuri’u a ranar zabe mai zuwa.

“An shirya taron ne domin shugaban kasa ya samu damar ganawa da sanatoci da mambobin tarayya wadanda ke kan kujerun su, da kuma masu shigowa bayan kammala zabe mai zuwa.

Shugaban na APC ya ce ya na da yakinin su ma sabbin ‘yan takara duk za su yi nasarar zaben da za a gudanar rana daya da na shugaban kasa, wato ranar 16 Ga Fabrairu mai zuwa.

Ya ce jam’iyyar APC ba ta jikara ko tsoron zabe, tunda dai kowane mai jefa kuri’a daya tilo kadai zai jefa.

Ya ce akwai alamun da ke nuna cewa duk APC za a zaba.

Oshiomhole ya ce taron ya bada damar sabbin ‘yan takara su gana da Buhari a karo na farko.

Sannan kuma an tattauna inda aka kwana da kuma inda za a tashi a batutuwan kamfen na kowace shiyyar sanata a fadin kasar nan.

Share.

game da Author