Dalilin da ya sa gwamnoni suka kaurace wa taron Kwamitin kamfe din Buhari – Oshiomhole

0

Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa dalilin da ya sa gwamnonin jihohin da jam’iyyar APC ke mulki ba su halarci taron kwamitin kamfe din shugaban kasa Muhammadu Buhari ba da aka yi a fadar shugaban kasa shine cewa suma a can jihohin su kai fa yayi zafi.

“Sanin kowa ne cewa wannan lokacin shine lokacin da kowa ke yakin neman jama’a saboda yadda siyasa da zabe ya kunnu kai. Kowa na can a jihar sa ne yana ganawa da jama’ar sa sannan da neman yadda zai samu kuri’un su.

” A dalilin haka ne nake kira ga mutane Najeriya da su karkato da hankulan su wajen ganin ci gaban da wannan gwamnatin ta kawo a shekaru uku da suka gabata sannan da kuma shirin da aka yi wa mutanen Najeriya da kasa baki daya idan suka ba wannan gwamnati dama a karo na biyu.

Gwamnonin jihohin kasar nan dake jam’iyyar APC suka kasa hallara taron kwamitin kaddamar da Kamfen din Buhari.

An yi taron ne a dakin taro dake fadar shugaban kasa inda a dalilin rashin zuwan gwamnmonin ya kawo rage murya a tsakanin wasu ‘ya’yan jam’iyyar da suka halarci taron.

Idan ba a manta ba shugaba Buhari ya bayyana cewa a kamfen din sa, tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ne wuka, shine nama wajen shirya kamfen din da wasu hidindimu da za a gudanar a lokacin kamfen din sa.

Kazalika, Buhari ya kara da yin kira ga mutanen Najeriya da kada su zabi gwamnonin da suka kasa biyan su albashi da wasu hakkokin su duk da dama da suka samu na

Wasu na ganin hakan na daga cikin dalilan da ya sa kila wasunsu suka kaurace wa taron ranar Alhamis.

Buhari zai ziyarci Kaduna, Bauchi da Gombe a karshen wannan mako da muke ciki domin kamfen din sa.

Share.

game da Author