Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya sake fitowa ya kare kan sa a bisa dalilan da ya ce su ne su ka sa ya ke goyon bayan tsohon mataimakin sa, Atiku Abubakar zama shugaban kasa a zaben 2019 da za a gudanar makonni biyu masu zuwa.
A cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar domin murnar zagayowar ‘Lagos Island Club’, Obasanjo ya kawo dalilai kwarara guda uku da ya kafa hujja da su.
A baya Obasanjo ya kira Atiku makaryaci kuma maras kunya, amma a yanzu ya ce ya yafe masa, kuma an wuce wurin, bayan da wasu mashahuran malaman addini suka shiga tsakani suka sasanta su.
A yau Laraba Atiku ya ce akwai abubuwa uku da Atiku ya yi da cancanci zama jagora kuma shugaba abin yi wa biyayya.
“ Na farko Atiku ba ya rufa-rufa, a matsayin sa na dan Adam, ya san inda ya ke da nakasu ko tasgaro. Bai taba boye wannan matsalar tasa ba, balle ya shafa wa kansa fentin da za a yi masa wani kallo na daban da ba yadda ya ke a zahiri ba. Atiku yadda ya ke haka kowa ya san shi bai taba ribbatar jama’a da karyar wai shi ya fi kowa zama nagari ba.
“ Masu irin halayen boye yadda su ke su na karyar gaskiya za ka ga su ne mayaudara, macuta, kuma ‘yan takifen da ke saurin kifar da jama’a.
“Atiku bai taba yi wa jama’a karyar cewa shi waliyyi ko ma’asumin da ba ya laifi ba ne.
“Abu na biyu kuma shi ne , kamata ya yi shugaba tilas ya zama mai gaskiya a kan sa da kuma a kan jama’ar da zai jagoranta. Ya kasance ya san inda ya ke da matsala kuma ya rika yarda ya na da matsalar ko nakasu ko tawaya a wannan bangare.
“ Kuma ya kasance idan ya yi kuskure ya na amincewa kuma ya na neman gafara. Amma ba wai a ce shugaba shi kullum bai yarda da ya yi kuskure ba, sai dai a ko yaushe ya rika dora laifin gazawar sa a kan wasu.
“ Duk mutumen da zai yi laifi ya yarda ya yi laifi har ya zo ya roki a yafe masa, to ka ga idan ka yafe masa, to kai ma sai Allah ya yafe maka. To irin wadannan su ne shugabanni abin zabi. Ba wai mutum ya yi laifi ba, kuma ya ki yarda da ya yi laifi, sannan kuma a zuciyar sa babu yafiya a tsakanin sa da wani.
“ Abu na uku shi ne, shugaba ya kasance ya san tushen matsalolin da ya ke son magancewa. Ya kasance ya na da hangen nesa, kuma ya kasance ya san hanyoyin da zai bi ya gina gwamnati tare da kwararrun da suka dace, ba ya tattara ‘yan hauragiya su kewaye shi a kan mulki ba.”
“ Don haka daga iyakar sani da kusancin da na yi da Atiku, duk ya na da waddanan rukunan cancantar zama shugaban kasa.” Inji Obasanjo.
Obasanjo ya ce daga Buhari har Atiku din duk su na da matsala, amma dai gara Atiku da Buhari.