Dalibai za su fi fahimtar darussan kimiyya idan ana koyar da su da harsunan su na asali – Inji Iyaye

0

Iyaye, malamai da wasu dalibai sun bayyana cewa dalibai za su fi fahimtar darussan kimiyya idan malamai na koyar da su da harsunan su gargajiya.

Sun yi wannan kira ne ranar Talata a hira da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Wani malami Hassan Toyin yace tabbas amfani da wannan dabara zai sa dalibi ya zamo mai hazaka musamman irin yara na karkara.

Wata uwa mai suna Hafsat Birnin ta kara da cewa yin haka zai yi matukar tasiri ga yara wajen gane karatu da kuma zama masu hazaka a makaranta.

Ta ce daliban dake zama a birane ne za su iya samun da tangarda wajen fahimtar karatun amma kuma a dan lokaci kadan za su saba.

Birnin ta yi kira ga gwamnati da a gudanar da bincike sosai kafina a fara amfani da wannan shiri musamman a birane.

Malamin makarantar sakandare ‘ Elite Stars’ dake Abuja Ibironke Babatunde ya ce amfani da dabaran zai taimakawa dalibai wajen rashin manta abinda ake koya musu.

” Na yi shekaru 16 ina koyar da dalibai sannan a wannan tsawon shekaru na gano cewa dalibai sun fi tunawa da abin da suka koya ne idan ana fassara abin da suke koyo din da harsunan su na asali ko kuma harsunan da su ka fi iyawa.

A karshe wata dalibar makarantar sakandaren Unity Collage dake karamar hukumar Tarka a jihar Benuwai Glory Modeva ta ce za ta fi kwarewa a darussa musamman lissafi idan malamanta na koyar da ita da harshen Tiv.

” Kowa koyan harshen Turanci yake yi saboda ba harshen mu bane a Najeriya sannan nafi gane karatu a lokacin da nake kauye saboda malamina da harshen Tiv yake koyar da ni.”

Share.

game da Author