DAKATAR DA ONNOGHEN: Abin da Buhari ya yi mulkin kama karya ne karara – Inji Atiku

0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya soki dakatar da babban mai shari’ar Najeriya Walter Onnoghen cewa yin haka mulkin kama karya ne Buhari yayi.

Idan ba a manta ba Buhari ya ya dakatar da babban mai shari’ar kasar nan Onnonghen a dalilin binciken da ake yi masa na kin bayyana kadarorin sa a lokacin da ya zama babban mai shari’ar.

An bayyana cewa Onnonghen ya ki fadin wasu daga cikin kadarorin sa wanda hakan karya dokar aikin gwamnati ne.

Sai dai kuma tuni har Buhari ya nada sabon Alkali a madadin sa.

Buhari ya nada Ibrahim Tanko a matsayin sabon babban mai shari’a da ya maye gurbin Walter Onnonghen.

Wannan aika-aika da Buhari yayi ya sa mutanen Najeriya na ta tofa albarkacin bakin su a kai da ya hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Atiku yayi tir da abinda Buhari ya yi sannan ya kara da cewa dole ne fa a yi maza-maza a kwabi Buhari domin yana neman ya maida hannun agogo baya a kasar nan.

Atiku ya kara da cewa, jingine dokar kasa da Buhari yayi sannan ya yi gaban kan sa nuni ne cewa mutanen Najeriya sun fada cikin mulkin kama karya a karkashin shugabancin sa.

Dokar Najeriya ta ba majalisar kasa ce ikon iya tsige babban mai shari’a na kasa wanda suma sai har an sami akalla kashi biyu bisa uku cikin su kafin hakan ya tabbata.

Majalisar Dattawa ba ta san abinda ke faruwa ba game da wannan shari’a domin fadar shugaban kasa bata taba yi mata magana a kai ba ballantana ace wai har ta yi wani abu akai.

Shi ko Buhari a hujjojin da ya bada na yin haka ya ce CCT dake bincikar shi Onnonghen ne suka amince masa da ikon da yayi amfani da shi ya dakatar da shi mai shari’ar domin basu damar iya bincikar sa bisa ababen da ake tuhumar sa da shi.

Bayan haka ita kanta kotun daukaka kara ta gargadi CCT kada ta kuskura ta ci gaba da sauraren wannan tuhuma na Onnonghen dake gaban ta domin ba hurumin ta bane amma dai duk haka yanzu dai sun zama tatsuniya.

Share.

game da Author