Dakarun Najeriya sun kashe mahara 21, sun kamo 17 a jihohin Zamfara da Katsina

0

Jami’in rundunar sojin Najeriya Clement Abiade ya ce dakarun sojin Najeriya sun kashe mahara 21, sannan sun kamo 17 a wani farmaki da suka kai maboyar ‘yan ta’addan a dazukan dake iyaka da Jihohin Zamfara da Katsina.

Bayan haka kuma dakarun sun ceto mutane 89 da aka yi garkuwa da su a jihohin Zamfara da Katsina.

Abaide ya sanar da haka ne ranar Talata inda ya kara da cewa rundunar ta kai wannan farmaki a ne tsakanin ranakun 22 da 28.

Ya kuma ce masu garkuwan sun tsare 55 daga cikin mutanen da suka sace ne a karamar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara.

Bayan haka Abaide yace rundunar ta kama wasu mutane biyu da maharan wajen kawo musu rahotanni kafin su kai hare-hare.

Wadanda aka kama sune, Musa Amadu da Auwalu Mutairu a haka yanzu suna nan suna tsare ana tuhumar su da samun bayanai daga wurin su.

Abaide yace an rasa rayukan faran hula 11 da dan banga daya a dalilin arangamar da rundunar ta yi da maharan.

” Ina kuma so in shaida muku cewa maharan sun sace mutane shida ne a kauyen Asoula dake karamar hukumar Tsafe ba a Birnin Magaji ba kamar yadda wasu gidajen jaridun ke yadawa cewa sun fi haka.

Share.

game da Author