‘Da ya tona asirin mahaifiyar sa bayan ta aike shi ya saka wa mahaifinsa guba a abinci

0

A ranar Litini ne kotun Mapo dake jihar Oyo ta gurfanar da wata mata mai suna Adenike Ayodele da ake zargin ta zubawa mijinta Adeshina guba a abinci da ruwan wankan sa.

Daya daga cikin ‘ya’yan da wadannan ma’aurata suka haifa ne ya bayyana haka a kotu.

” Mahaifiyata ta bani wani abu a bakar leda mai kama da hoda ta ce in zuba wa mahaifin mu a abinci da ruwan wankan sa sannan kada na fada wa kowa.

Yaron ya ce ya kasa aikata hakan sannan ya sanar da mahaifinsa.

Dama can Adenike ta nemi wannan kotun da ta raba auren ta da yake shekara 14 da Adeshina saboda rashin kula.

Adenike ta bayyana cewa mijinta Adeshina baya kaunar ya ga ta ci gaba a rayuwa sannan kulun sai ya lakada mata dukan tsiya.

” Idan na tambayeshi kudin abinci ko kuma kudin makarantar yara Adeshina zai mun duka sannan ya yi duk iya kokarin sa domin ganin ya rusa sana’ar da nake yi.

A dalilin haka Adenike ke neman kotu da ta raba auren ta ganin cewa ta gaji haka nan da zaman auren.

Shikuwa Adeshina y ace karya kawai Adenike ke yi masa a kotu.

” Ni magidanci ne dake kokari wajen kula da iyalinsa amma duk kokari na Adenike ba ta da godiyar Allah.

” A haka fa na daure nake zama da ita sai kwatsam yaro na ya fada mun cewa Adenike ta aike shi ya zuba mun magani a abinci da ruwan wanka na.

Adeshina yace ya sanar da dangin sa game da hakan sannan suma sun tabbatar da hakan a kotu.

A karshe alkalin kotun ya yanke hukuncin cewa Adenike ta kawo iyayen ta a zama na gaba da kotun za ta yi.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 27 ga watan Faburairu.

Share.

game da Author