Babban Jojin jihar Nasarawa Suleiman Dikko ya bayyana cewa yana gab da ya daina saka hannu a takardun bada izinin kama masu laifi idan jami’an tsaro basu gaggauta daukan mataki ba game da rage cinkoso gidajen yarin dake jihar ba.
Dikko ya fadi hake a ziyara da ya kai gidajen yarin dake jihar inda ya gani cewa gidajen yarin duk a cike suke makil.
Ya ce hakan na da nasaba ne da rashin gurfanar da masu laifi a a Kotu da ganin an gaggauta yanke musu hukunci.
” Bincike ya nuna mun cewa akwai wasu dake tsare kusan shekara hudu kenan ba tare da an gurfanar da su ba a gaban kuliya ba.
Dikko ya yi kira ga duk ‘yan uwan wadanda ke tsare da aka bada belin su da su gaggauta biyan kudaden belin ‘yan uwan su su zo su tafi da su. Sannan kuma ya kara yin kira ga kananan alkalai da su gajarta tsawon yanke hukuncin masu laifuka a kotunan su.