Cincirindon mahalarta taron gangamin kamfen na dan takarar Shaugaban Kasa a karkashin APC, kuma Shugaba Muhammadu Buhari, sun hargitsa filin wasan da ake taron ta yadda har Buhari ya fice ta bayan fili ba tare da ya yi jawabi ba.
Ya isa filin wasan bayan ya shafe kusan minti 30 jami’an tsaro na fama da dandazon jama’a, kafin su samu buda masa hanyar shiga ciki.
Wasu magoya bayan sai da ta kai har a saman motocin tawagar shugaban kasa suka rika hawa.
Ana cikin haka sai wasu gungun jama’a runduna guda suka antayo cikin fili, suka nufi dandalin da shugaban kasa zai yi jawabi.
Nan da nan aka fice da Buhari ta kofar da ake fita ta baya, ba tare da ya yi jawabi ba.
Shi ma gwamnan jihar, Simon Lalong da sauran manyan APC ba su damar gabatar da na su jawaban ba.