Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya sanar da dandazon magoya bayan jam’iyyar APC a garin Imo cewa gaba daya mutanen jihar sun yanke shawarar sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa mai zuwa.
” Mu a jihar Imo Buhari zamu zaba a zaben shugaban kasa, amma zaben gwamna kuwa ba za mu zabi APC ba domin haka kawai wani ba zai zo ya kakaba mana dan takara ba ba. Saboda haka mun riga mun yanke shawarar mu tuni.
Okorocha ya kara da cewa an samu ci gaban da ba a taba samun irin sa ba a jihar tun bayan dawowar dimokradiyya a 1999.
” Bayan wannan ci gaba da aka samu, akwai dayawa da aka samu a wasu sassan yankin Kudu Maso Gabas da ada babu irin su.
Ita kuwa uwargidan shugaban Kasa, Aisha Buhari a na ta jawabin, kira tayi ga mata da matasa da su tabbata sun zabi jam’iyyar APC da shugaba Buhari domin ci gaba da kwankwadar romon dimokradiyya da suke sha a yanzu.
Uwargidan mataimakin shugaban Kasa, Dipo Osinbajo ce ta wakilci Aisha Buhari a wannan gangami.
Wannan gangami shine na farko wanda bangaren kamfen din mata da matasa da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta kaddamar a makon da ya gabata.
Discussion about this post