Buhari zai sanar da sabon Sufeto Janar din ‘yan sanda

0

Idan dai ba samun canji na gaggawa aka yi ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai sanar da sabon Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya da zarar Sufeto Ibrahim Idris ya yi murabus ranar Talata.

A bisa kwararan majiya da PREMIUM TIMES ta jiyo daga fadar shugaban kasa da rundunar ‘yan sandan Najeriya, tuni shugaba Buhari ya amince da nadin Sufeto Abubakar Adamu a matsayin sabon shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Ranar Talata Sufeto Idris Ibrahim zai yi murabus da ga aikin ‘dan sanda bisa yawan shekaru.

” Tuni dai har sufeto Idris mai barin gado ya fara tattara kayan sa daga gidan sa mallakar gwamnati. Ina tabbatar muku da haka.” Haka majiyar mu a fadar shugaban kasa ya sanar mana.

Shi dai Abubakar Adamu dan asalin Jihar Nasarawa da aka fi kira da suna Adamu Mohammed Lafiya. Ya shiga aikin dan sanda a 1986.

Share.

game da Author