Buhari ya nada El-Yakub mai taimaka masa kan harkokin majalisar Tarayya

0

A bisa murabus din da mai taimakawa Buhari kan harkokin majalisar Tarayya Kawu Sumaila yayi shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Honarabul Umar Ibrahim El-Yaquk a madadin sa.

El- Yakub ya taba wakiltar Kano Municipal a majalisar tarayya daga 2003 zuwa 2007.

Kawo Sumaila ya hakura da aikin ne inda ya koma Kano domin takarar kujerar Majalisar Tarayya da ya taba yi a zabe mai zuwa.

Share.

game da Author