Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Tanko Mohammed sabon babban mai shari’a na kasa.
Ibrahim Tanko ya maye gurbin Walter Onnonghen ne da Buhari ya dakatar a yau Juma’a.
Buhari yayi wannan nadi ne a fadar shugaban kasa bayan ya saka hannu a dokar bashi ikon yin haka.