Buhari: Na cika alkawurran da na dauka a kamfen din 2015

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya cika dukkan alkawurran da ya dauka a lokacin kamfen din 2015 ga ‘yan Najeriya.

Ya yi wannan ikirarin ne a jihohin Imo da Abia, inda ya halarta jiya Talata a ci gaba da kamfen din da ya ke yi domin neman sake zaben sa a karo na biyu a zabe mai zuwa.

Jama’a sun fita duk kuwa da umarnin da kungiyar IPOB ta bayar cewa kowa ya zauna a gida.

Buhari ya je kamfen din tare da rakiyar tsohon gwamna Orji Uzo Kalu, Ogbonnaya Onu, Ken Nnamani, Niyi Adebayo da Chris Ngige da sauran su.
Shi ma shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshimhole ya na wurin kuma ya yi jawabi.

Buhari ya ce duk da faduwar darajar farashin danyen man fetur a zamanin mulkin sa, gwamnatin APC ta yi rawar gani matukar gaske.

Ya sake alkawarin cewa idan aka sake zaben sa, to kara inganta hanyoyin inganta rayuwar al’umma.

Ya ce an yi tinuna kuma an yi kokari wajen killace dukiyar al’umma, an inganta tsaro kuma an inganta tattalin arziki, sannan an dakile cin hanci da rashawa kwarai ainun.

Ya yi kira ga al’ummar jihar Abia su tabbatar APC ce suka zaba domin ta ci gaba da mulki a 2019.

Buhari in Abia State

Buhari in Abia State

Share.

game da Author