Gwamnatin Najeriya ta ware a cikin kasafin kudi na 2019 cewa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaba, Yemi Osinbajo za su kashe naira biliyan 1.461 wajen abinci da kuma zirga-zirga.
Bayanan da PREMIUM TIMES ta ci karo da su ne a Ofishin Tsara Kasafin Kudi suka tabbatar da haka.
Buhari zai kashe naira miliyan 250 a zirga-zirga cikin Najeriya, yayin da zai kashe miliyan 751 a zirga-zirgar kasashen waje.
Haka kuma shugaban zai ci abincin naira miliyan 98 da aka rigaya aka wasr a cikin kasagin kudin 2019.
Shi kuma ataimakin sa zai kashe naira milyan 301 a tafiye-tafiye, a cikin shekara daya, inda zirga-zirgar kasashen ketare zai lashe naira milyan 217, na nan cikin gida kuma zain kashe naira miliyan 83.
Wannan jimillar adadi ya haura naira milyan 937 da aka kashe a kasafin kudi na 2018.