Buhari ba shi da gaskiyar da ake tunani, gwamnatin sa ta ‘yan cuwa-cuwa ce -Inji Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba fa mutum nagari mai gaskiya ba ne kamar yadda ake ta kururuwa a kan sa.

Saraki ya ce gwamnatin Buhari gwamnati ce ta mahandama da kuma wawurar kudaden jama’a.

Da ya ke jawabi a Gidan Talbijin na Channels, a matsayin Saraki na Darakta Janar na Kamfen din Atiku, ya ce Buhari ya rungumi masu kashi a gindi ya goya, don haka kimar sa da kallon da ake yi masa na mai gaskiya, ta zube a kasa warwas.

“Ko shakka babu akwai marasa gaskiya a kewaye da Buhari. Idan da gaske Buhari ya na yaki da cin rashawa ne, ina mamakin yadda har yau an ki hukunta wadanda ake zargi da ke kewaye da shi.”

“ Matsawar ka na shugaba, amma ka ki bari a hukunta wadanda ke kewaye da kai, to wace nagarta kuma za a sake kallon ka na da ita?”

Da aka tambaye shi ko shi Buhari din ya na cuwa-cuwa? Sai ya ce gwamnatin sa gwamnatin cuwa-cuwa ce don haka idan ana yi ba ka hukunta masu yi, ai kamar ka amince ne, ko ka bayar da kofa.

Share.

game da Author