Boko Haram sun kashe sojoji takwas Geidam

0

A wani sabon turnukun fada, Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya takwas a Geidam, Jihar Yobe.

Majiyar cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa baya ga takwas da suka rasa rayukan su, da dama kuma sun ji ciwo, a harin wanda Boko Haram cike da motocin yaki samfurin A-kori-kura 12 suka kai da misalin karfe 6 na yamma.

Harin ya sa jama’a da dama tserewa daga gidanjen su.

Maharan sun rika jidar kayan miya da sauran nau’o’in kayan lamba su ka rika lodawa a cikin mota, daga baya kuma suka rika cinna wa shaguna wuta.

Sun kuma zarce har Babbar Kwalejin Fasaha ta Mai Idris Alooma Polytechnic, inda a can ma suka bude wuta.

Majiya daga bangaren sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa daya daga cikin sojoji takwas da aka kashe, ya na daga cikin jami’an tsaron da ke kula da tsaron babbar kwalejin. Hakan ya sa sauran suka tsere a lokacin gumurzun.

A cikin wata hira da PREMIUM TIMES ta yi da wasu sojoji a boye da a yau Juma’a, sun nuna matukar damuwar su ganin yadda har Boko Haram suka yi karfin-hali da kukan-kurar kutsawa ta yankin kuma har suka yi barna, a shi wannan yanki da aka girke sojoji a matsayin wata katanga ko babban bangon hana Boko Haram kai hare-hare a kudancin Kogin Komadogou-Yobe da ke bakin Tafkin Chadi.

Garin Geidam ya sha fama da hare-hare daga Boko Haram. Tun cikin 2011 mahara suka fara kai masa harin da har yau ba su daina kaiwa ba a bayan tsawon lokaci zuwa lokaci.

Geidam dai ba a cika kai hari a garin ba, kamar Bubi Yadi. Ana ganin saboda jajircewar da sojoji suka yi suka hana Boko Haram kai wa bakin kogi.

Sai dai kuma wannan ne karo na farko da aka kai wa sansanin sojoji a Geidam hari, wanda ke kan iyaka da Diffa, Jamhuriyar Nijar.
Har yanzu ba a san ko sojoji nawa ba ne suka tsere, amma dai an tabbatar da cewa suna da yawa.

An kwashe kimanin sa’o’i 12 ana fafatawa, tun daga ranar Laraba har zuwa ranar Alhamis.

PREMIUM TIMES ta kira wasu manyan jami’an sojoji, ciki har da Onyema Nwachukwu amma bai dauki waya ba.

Shi kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, Addulmalik Sunmonu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa duk wata tambayar da ake da ita, to a tuntubi sojoji.

Share.

game da Author