Boko Haram sun kashe mutane biyu a jihar Barno

0

Boko Haram sun kai wa kauyen Sajeri dake kusa da Maiduguri jihar Barno hari inda a dalilin haka mutane biyu suka rasa rayukan su.

Mazaunan kauyen sun bayyana cewa Boko Haram sun kai wa kauyen hari ne a daren Litini.

Wani mazaunin kauyen mai suna Mustapha Ali ya bayyana cewa Boko Haram sun sace kayan mutane, sun kona wasu gidaje sannan sun kashe mutane biyu a kauyen.

” Mun tsira ne a dalilin shiga dajin da muka yi.”

Bayan haka kwamandan rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ Benson Akinroluyo ya tabbatar wa manema labarai da aukuwan harin.

Bayanai sun nuna cewa Boko Haram sun fara kai wa kauyen Auno ne hari kafin suna shigo kauyen Sajeri.

Share.

game da Author