Boko Haram sun kai hari kauyen Magumeri, jihar Barno

0

A ranar Lahadi ne da karfe 6 na yamma Boko Haram suka kai wa kauyen Magumeri hari.

Kauyen Magumeri kauyen manoma ne dake da nisan kilomita 50 tsakaninta da garin Maiduguri.

Babu tabbacin adadin yawan da suka mutu da yawan wadanda suka sami rauni amma bayanai sun nuna cewa Boko Haram sun fara kai wa wannan kauye hari ne tun a ranar 25 ga watan Nuwambar 2017.

A dalilin wannan hari kuwa sojoji uku suka rasu sannan mutane shida suka sami rauni.

Rundunar sojin Najeriya ta zargi mazaunan kauyen da hada baki da Boko Haram wajen kawo wa kauyen hari sai dai mazauna kauyen sun musanta aikata haka.

Share.

game da Author