BOKO HARAM: An tura sojojin sama mata yin gumurzu da ’yan ta’adda

0

Rundunar Sojojin Sama ta Kasa, NAF ta bada sanarwar tura zaratan sojojin sama mata da ake kira Mata Zaratan Yaki zuwa yankin Arewa maso Gabas domin yin gumurzu da Boko Haram.

Babban Hafsan Hafsoshin Sama, Sadique Abubakar ya ce a yanzu haka akwai da dama da ke gwabza yaki tare da zaratan musamman a wurare daban daban.

Ya shaida wa PRNigeria cewa NAF babu ruwanta da nuna bambanci, kuma ta na kara cicciba kowane jinsi domin ya samu karin horo da goguwar kwarewa a aikin sa.

“ Mu na kiran su da suna Mata Zaratan Yaki ne saboda sun horu, sun gogu kuma sun samu kwarewa wajen iya gwabza gumurzun fada a duk inda aka kai su, ko kuma inda suka samu kan su.

“ Su ma wadannan matan kamar abokan aikin su maza su ke. Sun kware sosai wajen kakkabe abokan gaba masu ta’adda musamman wajen iya kai farmaki daga sama, tare da bada dauki ga sojojin da ke gumurzu da Boko Haram a kasa.

Ya ce sun samu horo a cikin Najeriya da kuma kasashen Turai.

Share.

game da Author