BINCIKE: Akalla mutane miliyan 14.3 na ta’ammali da muggan kwayoyi a Najeriya

0

Sakamakon binciken cibiyar yaki da sha da Ta’ammali da muggan kwayoyi na majalisar dinkin duniya (UNODC), NBS, cibiyar (CRISA) da EU ya nuna cewa akalla mutane miliyan 14.3 na ta’ammali da kwayoyi a Najeriya.

EU ta gabatar da sakamakon wannan bincike ne ranar Talata a Abuja inda ta kara da cewa adadin yawan mutanen dake Ta’ammali da Kwayoyi a kasar nan ya fi adadin yawan mutanen dake wasu kasashen turai.

Sakamakon ya kuma nuna cewa ‘yan shekaru 15 zuwa 64 ne suka fi shiga cikin wannan matsalar sannan a cikin mutane hudu dake fama da wannan matsalar daya mace ce.

Bayan haka binciken ya kuma kara nuna cewa kwayoyin da amfani da su ya zama ruwan dare a kasar nan sun hada da hodar ibilis, tabar wiwi, kayar tramadol da maganin tari kodin sannan kuma a Arewacin Najeriya ne abin yafi muni.

Da yake yaba wa kokarin binciken da EU ta gudanar karamin ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya ce abin takaici shi ne yadda mafi yawan mutanen dake fama da matsalolin shan kwayoyi basu samun kula a asibitocin kasar nan.

” Tabas a kwai asibitocin dake kula da irin wadannan mutane amma basu da yawa sannan wadanda ake da su sun fi bada karfi wajen kula da maza ba mata kuma gashi farashin samun magani na da tsada.

” Abin da ya rage mana shine zantar da matakan kawar da wannan matsalar ganin cewa sakamakon wannan binciken ya zama mana abinda zai sa mukarkata zuwa ga wurin yin haka.

A karshe Sun ce ci gaba da wayar da kan mutane game illar dake tattare da shan miyagun kwayoyi na da mahimmanci, kara yawan asibitocin kula da masu fama da matsalar amfani da miyagun kwayoyi da kafa dokar hana bude shagunan siyar da magani ba tare da yin rajista ba na cikin matakan da za su rage wannan matsala da ake fama da su.

Share.

game da Author