A safiyar Asabar din nan ne aka sanar da rasuwar babban wan gwamnan jihar Kaduna, AVM Rufai.
Kakakin gwamnan Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a madadin gwamnan, inda ya ce AVM Rufai ya rasu a asibiti a Abuja ranar Asabar.
Za a yi jan’izan sa a masallacin Sultan Bello da karfe 4 na yamma.
Marigayi AVM El-Rufai ya rasu yana da shekaru 71 sannan ya bar mata daya da ‘ya’ya 6.
A cikin kannin sa akwai Bashir El-Rufai da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai.
Discussion about this post