Ba zan damu ba idan aka kayar da APC a Zamfara ba -Sanata Marafa

0

Sanata Kabiru Marafa na APC daga jihar Zamfara, ya dora alhakin halin da jam’iyyar APC ta shiga a jihar a kan ita kan ta uwar jam’iyyar ta APC.

Ya kara da cewa ko a jikin sa ba zai taba damuwa ba idan APC ta fadi zabe a jihar ta Zamfara.

Wannan furuci na sa ya zo kwanaki kadan bayan Babbar Kotun Tarayya ta jaddada amincewa da INEC kan hana APC shiga zabuka a jihar Zamfara.

Tun a cikin watan Okotoba da ya gabata ne INEC ta ce kada ma APC ta bata lokacin tura mata ‘yan takarar kowane zabe daga jihar Zamfara, domin ba za ta shiga zaben ba.

INEC ta ce ta hana APC shiga zabe a jihar Zamfara ne saboda ta tsaya ta na fama da rigingimu har wa’adin gudanar da zaben fidda gwani ya wuce ba su fidda ‘yan takara ba.

Ta ki amincewa da zaben da gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya ce ya gudanar. INEC ta ce ba shi da hurumin shirya zaben fidda-gwani, aikin Kwamitin Gudanarwa na uwar jam’iyya ta kasa ne.

Sai dai ita kuma Babbar Kotun Jihar Zamfara ta ce an yi zabe, don haka ta nemi INEC ta amince da jam’iyyar APC ta mika sunayen ’yan takarar ta.

APC BA FA BA ADDINI BA CE – MARAFA

Da ya ke zantawa da manema labarai a Majalisar Tarayya jiya Talata, Marafa ya ce akwai iyar mizanin da mutum zai iya yi wa Majalisa ko jam’iyya biyayya.

“Biyayya ta gaba daya na mika ta ga Allah ne, sai kuma jama’ar da na ke wakilta. Amma APC ai ba addini ba ce.

“Idan APC ta ga dama ta tsaida rubabi-rubabin dan takara, to zan amince musu da hakan amma dai wannnan hauragiyar ba a ni za a yi ta ba.”

Ya ce tun farko APC ce ta haifar da matsalar saboda ta shaida wa wakilan zabe ga wanda za su zaba.

“ APC ta ce wa Sanatoci mu zabi Ahmed Lawan. Duk da yawancin mu mun fi kusanci da Saraki, amma a haka muka bi umarnin su. Amma wadanda suka yi wancan danyen hukunci, sai aka wayi gari kuma sun koma sun hade mana kai, kun kware mana baya.

Marafa ya ce su ne din dai suka haddasa rikici a cikin APC ta jihar Zamfara.

“Sanata Adamu Aliero ne kan wa uwar gamin tabbatar da cewa Ahmad Lawan bai zama shugaban majalisar dattawa ba. Saboda shi dama dan kwangila ne.

Marafa ya yi kiran da gwamna Yari ya sauka daga mulki. Sannan a gurfanar da shi, a daure shi, saboda ya ci amanar kasa.

“Idan Yari ya isa ya sauka daga gwamna, na sauka daga sanata mu je mu tsaya zabe. Idan har ya samu kai ko da kuri’a 10 bisa 100 ce, to na yarda ya kayar da ni.

Share.

game da Author