Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayayyana cewa tunda an ce da babu gara akwai ko da babu dadi, to har gara Atiku sau dubu da Buhari.
Obasanjo ya bayyana haka ne a cikin wata hira da aka yi da shi a Gidan Radiyon BBC sashen ‘Pigin English’, na gargaliyar Turanci.
A hira ya kara da cewa kada a yi tunanin cewa Atiku shi ne mafita, amma dai shi ya tabbata idan ya hau mulki sai ya fi Buhari tabukawa sau dubu bayna kuwa ada ya rika ukar Atiku cewa dan wuru-wuru ne, kuma ba abin bai wa amana ba ne, yanzu kuma ya koma ya na goyon bayan sa.
Shi dai Obasanjo ya dawo daga rakiyar Buhari, wanda ya goyi baya a zaben 2015. Ya kuma zargi Buhari da nuna kabilanci da bangaranci.
Sannnan kuma ya kara da cewa barayin da ke cikin gwamnatin Buhari ba kurkuku kadai za a tura su ba idan aka fallasa su. Ya ce wuta ce makomar su.
Daga nan kuma sai buga misali da irin mutanen dake cikin gwamnatin Buhari da wadanda ke kewaye da shi, cewa duk mai hankali zai yarda ay Atiku zai fi Buhari kokari idan ya hau mulki.
“Masu cewa ai a baya na ce Atiku ba mutumin kwarai ba ne, to sai kuma su duba baya ai na ce Buhari ne mafitar Najeriya, amma aka yarda da ni, to ga shi ashe babu abin da ya sani, sai badambadama kawai ya ke ta yi.”
Obasanjo ya ce Buhari ya na jan akalar kasar nan zuwa wani kwazazzabo mai hatsari.
“Ka na shugaba amma kuma ba ka amince da sauran ‘yan wasu yan kuna ka ba su mukamai masu muhimmanci a kasa ba. To wane irin shugaba ne kai?”
Obasanjo ya ce bai kamata a ce shugaban kasa ne ke koyar da irin wannan darasin ba, domin ya na koya wa ‘yan baya mummunan darasi ne kenan.