Dan takarar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya nada tsofaffin gwamnonin jihohin Kaduna da Jigawa, Sule Lamido, da Ahmed Makarfi, Kakakin majalisar Tarayya, Yakubu Dogara da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu a mukamai.
Atiku ya nada Sule Lamido shugaban kwamitin dattawa na kamfen din.
Kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya sanar da haka sannan ya kara da cewa Atiku ya nada Abubakar Baraje a matsayin maitaimaka wa Darektan Kamfen din sa Bukola Saraki a matsayin babban mai bashi shawara.
Haka shima Doyin Okupe zai taimaka wa Saraki kan harkokin yada labarai.
Idan ba a manta ba mutane sun yi ta tofa alabarkacin bakunan su game da salon kamfen din Atiku din inda ake ganin yayi watsi da wasu daga cikin manyan ‘yan siyan jam’iyyar yana abinda shi yaga yayi masa dadai. Musamman mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da aka dauka shine Atiku zai zaba mataimakin sa kawai sai ya ji a salan sa, Atiku yayi gaban kan sa ya zabi Peter Obi.