APC ta nada tsohon gwamnan da ke kurkuku cikin Majalisar Kamfen Gwamnan Filato

0

Jam’iyyar APC ta nada tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye da ke daure a kurkuku a cikin Majalisar Kamfen din sake zaben Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato.

A yanzu dai Dariye na can a kurkuku daure, a Kuje, Abuja, inda ya ke zaman kaso na daurin shekaru goma.

Ya fara wa’adin sa tun a cikin watan Yuni, 2018.

Dariye wanda kuma shi ne Sanata mai wakiltar Filato ta Tsakiya, an same shi da laifin karkatar da naira bilyan 1.7 na tallafin magance zaizayar kasa a lokacin da ya ke gwamna, tsakanin 1999 zuwa 2007.

Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Filato, Yakubu Dati ne ya bada wannan sanarwar ta nadin da aka yi wa Dariye a cikin kwamitin kamfen na gwamna Lalong.

Sai dai kuma ba a san ta yadda wanda ke tsare a kurkuku zai yi wa gwana Lalong kamfen daga Kuje, Abuja ba.

Duk da ya na tsare a kurkuku, har yanzu Dariye ya na da karfin siyasa a Filato ta Tsakiya, domin babu mai bakin fada a ji kamar sa.

Kakakin Yada Labarai na Gwamna Lalong ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa babu wani laifi don an nada Dariye a cikin ‘yan kwamitin kamfen.

“Domin a yanzu dai Dariye ya daukaka kara, to wa ya sani kila ma Kotun Koli ta wanke shi, ya fito ya ci gaba da kamfen din sa?” Inji Kakakin Gwamna, mai suna Mark Longyn.

Ya ci gaba da cewa ita siyasa ai harka ce ta mutanen karkara, tushen da kowane dan siyasa ya fito. Kuma Dariye mutum ne mai jama’a sosai, mai fada a ji kuma a bi umarnin sa.

“Dariye ya daukaka kara, kuma har yanzu dai shi ne Sanata na Filato ta Tsakiya, kujerar sa na nan daram, ba a ce ta zama mai rabo ka dauka ba.”

“Kai bari na shaida muku, daga kurkuku idan Dariye ya sake tsayawa takara, to ko bai fito ya yi kamfen ba sai ya ci zabe.

“Domin tarihi ya nuna mutane sun ci zabe alhali su na kurkuku a tsare. Sanata Iyiola Omisore da tsohon gwamnan Abia, Orji sun ci zabe a lokutan da su ke a tsare a kurkuku.” Cewar Longyn.

Share.

game da Author