Anyi garkuwa da mata masu shayarwa, amarya, yara da wasu 26 a garin Zurmi, jihar Zamfara

0

Jihar Zamfara dai ta yi kaurin suna wajen ayyukan ta’addanci musamman yin garkuwa da mutane a yankin Arewa.

A ranar litinin mahara sun far wa garin Zurmi dauke da manyan bindigogi suna harbi ta ko-ina inda bayan haka suka yi garkuwa da mutanen garin har su 26.

Wani malamin makarantar Sakandare Falalu Ashafa daya bayyana cewa an tafi da matar sa, mahaifiyar sa, ‘ya’yan sa biyu da mai taya matar sa aiki.

Bayan nan, sun yi garkuwa da wasu mata dake shayar wa da mutane 26.

Kakakin rundunar ‘Yan sanda jihar Zamfara ya bayyana cewa akalla mutane 13 ne suka tabbatar sun bace a wannan hari da masu garkuwa suka kawo gari Zurmi din.

Bayan haka, tuni har jami’an mu sun fantsama cikin wannan daji tare da wasu ‘yan banga domin shiga cikin kungurmin dajin.

Idan ba a manta ba Karamar hukumar Zurmi da Birnin Magaji ya na daga cikin kananan hukumomin da ayyukan ta’addancin da garkuwa da mutane ya yi wa katutu.

A kwanakin baya masu garkuwa suka sace wata matan aure da sai da ta yi kusan mako biyu zaune tare da su. Daga baya ne dai aka sake ta bayan an biya kudin diyya.

Share.

game da Author