Mataimakin gwamnan jihar Taraba Haruna Manu ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun sakataren yada labaran gwamnan jihar Darius Ishaku, Hassan Mijinyawa ranar Laraba a hanyarsa ta zuwa Kamfen Gembu, Karamar Hukumar Sardauna.
Uwargidan Mijinyawa, Sekina Mijinyawa ta tabbatar da sace mijin nata da aka yi inda ta kara da cewa mijinta ya bar gida da karfe bakwai na safiyan Laraba zuwa tsaunin Mambila wajen Kamfen din gwamna Dairus.
Sekin ta roki masu garkuwan da su tausaya mata su saki mijinta da suka tafi da.
Yusuf Garba daya daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya daga tarkon masu garkuwan a wannan rana ya bayyana cewa masu garkuwan sun kama mutane da dama wanda a ciki har da wani bature dake kula da wani sansanin ‘yan gudun hijira.
” Bayan sun kammala kwace ababen dake hannun mutanen da suka kama sai suka kada su suka yi daji da su.”
A karshe kwamishinan ‘yan sanda jihar David Akinremi, yace tuni sun fara gudanar da bincike domin kwato wadannan mutane da aka kama.
Discussion about this post