An yi garkuwa da mutane 7 a gidan kallon kwallo a Zamfara

0

Masu garkuwa har su 20 sun yi garkuwa da matasa masu kallon kwallo a wani gidan kallo dake garin Birnin Magaji, Jihar Zamfara.

Kamar yadda mahaifin wasu yara biyu da aka sace cikin wadanda aka tafi da su ya bayyana cewa bayan ‘ya’yan sa da aka tafi da an waske da mai gidan kwallon.

” Maharan har su 20 sun far wa wannan gidan kwallo ne sanye da kayan sojoji da na ‘yan sanda.

” Da yawa an dauka jami’an tsaro ne masu Kula da wannan yanki ashe masu garkuwa ne.

” Bayan sun dan yi shawagin su sai su ka fada ciki suka ware da matasa 7.

BIRNIN MAGAJI

Garin Birnin Magaji da nan ne garin ministan tsaro, Mansur Dan-Ali ya yi kauri suna wajen ayyukan ta’addanci.

Akalla mutanen kauyuka sama da 30 ne ke samun mafaka a garin Birnin Magajin. Inda kusan dukkan su na kwana ne a filin Allah Ta’ala. Wasu a karkashin itatuwa, kango da filayen wasa.

Share.

game da Author