Wasu mazaunan kauyukan dake karamar hukumar Safana sun bayyana cewa a ranar 19 ga watan Disamba wasu ‘yan bindiga sun sace wasu mutane 20 a wasu kauyuka dake karamar hukumar.
Wani mazaunin kauyen da baya so a fadi sunan sa ya fadi haka wa wakilin PREMIUM TIMES.
Yace maharan sun yi garkuwa da mutanen ne a hanyar su na dawowa daga daurin aure da aka yi a kauyen dake kusa da na su.
” Bayan an kammala daurin auren ne fa mutane suka dunguma cikin motoci biyu zuwa gida sai wadannan mahara suka far wa motocin. Su sa kowa ya fito daga cikin motar sannan suka bukaci kowa ya sallama musu wayar sa da kudin da ke jikin sa.
” Da yake matafiyan kauyawa ne kusan dukkan su basu da kudi da waya kwai sai suka tattara su duka su dunguma dasu cikin kungurmin da ji.
Akwai wadanda suka arce a wannan lokaci amma daya daga cikin su ya tsira ne da harbin bindiga har biyu a kafadar sa.
Maharan sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 kudin diyya inda daga baya suka rage zuwa miliyan 40.
A haka dai mutanen wadannan kauyuka suka shiga neman taimako daga juna su domin tara wani abu da za aba wadannan mahara da suka sace mutanen.
A dalilin haka mazaunan suka yanke hukuncin kai kukan su ga Allah domin samun mafita.
Kakakin ‘Yan sandan jihar Katsina Gambo Isa ya ce rundunar bata da masaniya game da wannan abu da ya faru a wannan kauye sai dai za su ci gaba da bincike.
Duk da wannan batu da Gambo yayi na rsahi sani, gwamnan jihar Aminu Masari ya tabbatar da aukuwar haka, yana mai cewa Jihar Katina fa ta fada cikin wani mawuyacin hali na rashin tsaro.