An samu rahotannin fyade 105, na kisa 168 cikin 2018 a Kano -’Yan sanda

0

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce a cikin shekarar 2018, an samu rahotannin aikata manyan laifuka 337 a jihar Kano, wadanda suka hada da laifin kisan kai 168 da kuma na aikata fyade 105.

Ta bayyana haka ne a cikin rahoton ta na karshen shekara, wanda ta aiko wa PREMIUM TIMES a jiya Laraba.

Kakakin rundunar Magaji Majiya, ya ce an kuma samu rahoton satar motoci har sau 34 duk a cikin 2018.

Sai dai kuma ya ce jihr ta samu raguwar aikata manyan laifuka a 2018, idan aka yi la’akari da 337 da ta samu rahoto, maimakon 601 da rundunar ta samu cikin 2017.

Ya kara da cewa a cikin 2018, an kama ‘yan daba har 2487, kuma an kwace makamai masu dama a hannun su.

An kuma samu rahotannin satar garkuwa da mutane har sau 42 a jihar Kano cikin 2018. A 2017 dai an samu rahoton garkuwa a jihar sau 21.

Share.

game da Author