Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban jam’iyyar APC na jihar Abia, Donatus Nwankpa.
Rundunar Yan sandan Jihar ta Abia ta ce an yi garkuwa da shi ne tun a ranar Litinin, kwanaki biyu da suka gabata.
Kakakin Yada Labarai na ‘yan sandan Abia, Geoffrey Ogbonna ya shaida wa Kamafanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN cewa su na sane da labarin sace shugaban jam’iyyar.
Ya nuna rashin jin dadin sace shi da aka yi a ranar jajibirin da Buhari zai kai ziyara a jihar.
Shi ma kakakin yada labarai na jam’iyyar APC na jihar, Benedict Godson, ya shaida wa manema labarai cewa an sace Nwankpa da misalin karfe 11 na rana a ranar Litinin, a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa garin Aba daga Umuahia.
An sace shi tare da daya daga cikin hadiman sa, amma daga baya sun saki hadimin na sa, suka rike shi.