Likitocin jami’ar Berkeley (UC) da na jami’ar California, San Francisco (UCSF) a kasar Amurka sun gano maganin rage illolin da yiwa mutum mai dauke da cutar daji ‘Chemotherapy’ ke yi.
Chemotherapy na’ura ce da ake amfani dashi wajen kashe kwayoyin cutar daji a jikin mutum.
Bayanai sun nuna cewa a dalilin amfani da hanya na kashe kwayoyin cutar wasu bangarorin jikin mutum kan sami matsala.
Wadannan matsaloli kuwa sun hada da tsinkewar gashin kai da jiki, rama, samun matsala a hanta da sauran su.
Domin kawar da irin wadannan matsaloli ne likitocin suka gudanar da bincike domin rage wadannan matsaloli da kuma wahalar da masu fama da wannan cutar ke fadawa.
Likitocin sun ce maganin da suka gano din magani ne da zai taimaka wajen hana bangarorin jikin masu fana da wannan cuta shiga wani hali yayin da suke ake musu amfani da wannan hanya na maganin cutar, wato ‘Chemotherapy’.