Korarren shugaban Hukumar Inganta Manyan Makarantu, wato TETFund, Abdullahi Baffa, ya bayyana cewa an kore shi ne saboda Ministan Ilmi, Adamu Adamu ya zarge shi da karbar rashawa daga manyan makaratun kasar nan.
PREMIUM TIMES ta ruwaito korar Baffa da aka yi, tun a ranar Litinin, amma ba a fadi dalilin korar ta sa ba.
An maye gurbin sa da Suleiman Bogoro, wanda a baya aka kore shi aka nada Baffa a cikin 2016.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito Baffa na cewa Adamu ya aiko wani makusancin dan kwangila inada ya zarge shi da karbar kashi 10 daga cikin naira bilyan 200 da TETFund ta raba wa manyan makarantun gaba da sakandare.
Ya zarge shi da cewa ai idan ma kashi 1 bisa 100 na kudin aka ba shi, to ya karbi naira bilyan 20 kenan a matsayin rashawa.
Amma Baffa ya shaida wa BBC Hausa cewa bai taba karbar ko sisi a matsayin cin hanci ba.
“Na yarda idan an kama ni da laifi ya yanke min hukuncin kisa.” Inji Baffa.
PREMIUM TIMES ta kasa samun Adamu da kakakin yada labaran sa. Shi kuma karamin ministan ilmi, ya ki cewa komai dangane da batun.