Hukumar kula da abinci da magunguna na kasa (NAFDAC) ta yi kira ga mutane kan amfani da man dake canza launin fatar jikin mutum cwwa hakan na haddasa cutar daji da na Koda.
Shugaban hukumar Moji Adeyeye ce ta yi wannan kira inda ta kara da cewa amfani da irin wannan man na da illa matuka a jikin mutum.
Adeyeye ta ce yin wannan kira ya zama dole ganin cewa hukumar ta gano sinadarin ‘Glutathione’ da dama da ake amfani da su wajen sarrafa irin wannan man da aka shigo da su kasan cewa wannan Sinadari na illata fatar mutum.
” A yanzu haka abin ya zama ruwan dare ga mutane domin ba mai ba ma kawai har kwayar wannan sinadari ana sha domin a canja launin jiki.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne wani babban Darektan da ke kula da sashen gwaje-gwajen magunguna a babbar asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan, Ganiyu Arinola ya yi kira ga gwamnati da ta saka dokar hana shigowa da man dake canja launin fatar mutum kasar nan.
Ganiyu ya ce rashin sani da kishin bakin fata ne ya sa mutane ke amfani da man da ke canja launin fatarsu. Sannan da saukin da yake da shi ya sa babba da yaro ke amfani da shi a kasar.
Ya ce amfani da irin wadadan mai na da matukar illa ga jikin mutum domin suna rage karfin garkuwan jikin mutum sannan yana kuma kawo cutar daji.
Ganiyu Arinola ya yi kira ga gwamnati da gidajen jaridu da su yawaita yin tallace- tallace da zai wayar wa mutane kai game da illolin da ke tattare da amfani da wadannan mai.