Jiya ne sabon Cif Jojin da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada, Ibrahim Mohammed ya rantsar da alkalai 250 da za su saurari kararrakin da ka iya biyo bayan gudanar da zaben 2019.
Sai dai kuma abin mamaki da nuna damuwa, shi ne mai shari’a daya ne kacal daga manyan alkalan Kotun Kolin Najeriya ya halarci taron rantsar da alkalan sauraren kararrakin zaben.
Saura 15 duk sun kaurace wa taron. Hakan ya biyo baya ne sanadiyyar tirka-tirkar dakatar da Cif Joji Walter Onnoghen da Buhari ya yi, ba tare da mika bukatar yin haka ga Majalisar Dattawa ba.
Wannan mataki ya janyo wa Buhari tsangwama a cikin gida har ma da Amurka da Tarayyar Turai gaba daya.
A jiya Asabar ne sabon Cif Joji ya rantsar da alkalan shari’un zaben, inda ya hore su da su yi aiki tare da tsoron Allah da kuma alkawarin za su kara tsarin mulki da dokokin kasa kamar yadda dokar Najaeiya ta rattaba.
Ya ce fannin shari’a na cikin wani mayuwayacin hali, don haka su nuna ba sani ba sabo tare da gudanar da aiki cikin gaskiya da adalci, ba tare da son kai ko bangaranci ba.
Ya ce akwai nauyi kan shugabannin kwamitin alkalan da mambobin su wajen sake dawo da martanar fnnin shari’a a kasar nan.