ALKALAMI YA BUSHE: Oby ba za ta iya janye wa daga takarar shugaban kasa ba – Hukumar Zabe

0

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa Oby Ezekwesili ba za ta iya janyewa daga takarar shugaban kasa ba cewa lokacin yin haka ya riga ya wuce.

Kakakin hukumar Rotimi Oyekanmi ya sanar da haka ranar Alhamis a Abuja.

Oyekanmi ya ce idan ba a manta ba hukumar ta tsayar da ranar 17 ga watan Nuwambar 2018 a matsayin ranar da duk ‘yan takarar shugabancin kasa da ‘yan takarar majalisar dokoki ta kasa za su fice ko kuma jam’iyyar su ta canja su.

Ya ce da zarar wannan rana ta wuce babu dan takaran da zai iya ficewa ko kuma a yi musanyan sa domin zuwa yanzu ma har an shirye shirye a hukumar yayi nisan gaske.

Idan ba manta ba Oby Ezekwesili ta janye daga takarar shugaban kasa ne da safiyar Alhamis inda ta bayyana haka a shafinta na twitter a sannan ta ce ta janye daga takarar ne domin ta gina gagarimar gamayyar wayar wa jama’a kai ta yadda za a guji jam’iyyu biyu din nan masu karfi, wato APC da PDP a lokacin zabe, har a kayar da su.

Oby ta ce ta yi tunanin daukar wannan mataki ne biyo bayan abubuwan da suka wakana yayin makabalar da yi tare da wasu ’yan takarar shugabancin kasa a makon da ya gabata.

Ta ce akwai bukatar a wayar wa ‘yan Najeriya kai cewa ba fa za a iya ci gaba ba, har sai an kawar da gungun ‘yan jam’iyyar APC da PDP.

Kakakin yada labarai na Oby, mai suna Ozioma Ubabukoh, ya tabbatar da janyewar da Oby ta yi.

Sai dai kuma jam’iyyar ta ACPN ta bayyana cewa ficewar Oby bai dada ta da kasa ba cewa dama can tayi amfani da jam’iyyar ce wajen samun kudaden gudunmawa daga kungiyoyi da wasu mutane. Tuni har jam’iyyar ta bayyana cewa APC za ta yi a azaben shugaban Kasa.

Share.

game da Author