Fitaccen dan wasan fina-finan Hausa, da aka yi wa lakabi da ‘Sarki’ wato Ali Nuhu ya jinjina wa masoyan sa sannan ya gode masu bisa cika shekaru 20 da yayi yana gwagwarmaya da farfajiyar Kannywood da fina-finan kasar nan.
Ali ya mika godiyar sa ga duk wadanda suka faro harkar tare a 1999 zuwa yanzu da kuma wadanda suka dafa masa ta kowacce hanya a tsawon wannan lokaci.
Ali Nuhu yayi fice a farfajiyar fina-finan Hausa matuka da wasu da dama suke ganin ba a taba dan wasa a wannan karnin ba kamar sa ba.
A saboda gogewar sa da maida hankali ga sana’ar sa har lakabi aka yi masa da ‘Sarki’.
Cikin irin gudunmawar da ya bada a farfajiyar fina-finan Hausa, har da koyar da ‘yan wasa masu tasowa da dafa musu inda kusan dukkan su da suka jingina da shi yanzu sun zama fitattu a harkar ba a Kannywood ba har da kasa baki daya.
Cikin wadanda Ali Nuhu ya goya, akwai fitacciyar yar wasa. Rahama Sadau da a yanzu babu kamarta a farfajiyar Kannywood da Nollywood. Rahaman tayi ficen da har a kasashen duniya sunan ta ya karade duk a bisa goyon Ali Nuhu.
Bayan ita akwai Nafeesat Abdullahi, Zaharadden Sani, Nuhu Abdullahi, da wasu da dama.
Ali ya karbi kyaututtuka da dama da babu wani dan wasan Kannywood da ya taba samun irin wadanan karramawa ba a Arewacin kasar nan ba har daga kasashen Turai, Amurka da India.
Ali ya fito a fina-finan Hausa sama da 1000 sannan ya fito a manyan fina-finan Turanci sama da 200 a tsawon shekaru 20 da yayi zuwa yanzu yana harkar.
Ali yana da aure da ‘Ya’ya biyu sannan shi ne ya ke bi wa Rahama Sadau a yawan mabiya a shafin Instagram.
Discussion about this post