Akwa Ibom ta kashe Naira biliyan biyar wajen siyan kayan aiki a asibitocin jihar

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Akwa Ibom Dominic Ukpong ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan biyar wajen siyo ingantattun kayan aiki a asibitin Ibom da wasu asibitoci dake jihar.

Ukpong ya fadi haka ne yayin da cibiyar din ‘Divine Mandate Campaign’ ta kai wa basaraken Eket Etim Abia ziyara.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin inganta aiyukkan wannan asibiti don samar wa mutanen jihar kiwon lafiya mai nagarta.

” Idan ba a manta ba gwamnatin da ta gabata ta kaddamar da wannan asibiti ne batare da an kammala ginata. Zuwan wannan gwamnayi ke da wuya, ta maida hankali wajen ganin an kammala wannan gini sannan an wadata asibitin da kayan aiki domin mutanen jihar.

Ukpong ya kuma kara da cewa gwamnati ta kammala gyara wasu asibitoci a jihar kamar su asibitin Ituk Mbang, asibitin Immanuel, babbar asibitin Etinan, asibitin Ikono da asibitin Awa.

” Cikin gyaran da gwamnati ta yi wa wadannan asibitocin sun hada da samar da motocin daukan marasa lafiya sannan da daukan kwararrun ma’aikatan da zu kula marasa lafiya.

A karshe Ukpong ya yi kira ga mutanen jihar da su zabi gwamna Emmanuel a karo na biyu domin ci ga a da kwankwadar romon dimokradiyya a jihar.

Share.

game da Author