Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ya bayyana cewa kamata ya yi masu karajin sake bukatar sake fasalin Najeriya su tunkari shugabannin Arewa, su tabbatar musu cewa akwai alheri mai yawa da za su amfana idan aka sake fasalin Najeriya.
Ya ce ba wani abu su ke tsoro ba sai gudun kada su daina samun kudin fetur zuwa Arewa idan aka sake fasalin Najeriya.
A cikin wata tattauna ta musamman da ya yi da PREMIUM TIMES, Ekweremadu ya ce tilas sai an sake fasalin kasar nan, idan har ana so tattalin arzikin kasar nan ya ci gaba.
Ya ce akwai matukar muhimmanci a zauna tare da shugabannin Arewa kuma a kuma wayar da talakawan yankin cewa za su fi cin moriyar zamantakewar su tare da sauran yankunan kasar nan idan aka sake fasalin Najeriya.
Ya kuma ce akwai bukatar a ci gaba da zama tsakanin shugabannin Kudanci da na Arewacin Kasar nan, domin a kara fahimtar juna a amince wa juna sosai da sosai.