Matashin dan takarar majalisar jihar Kano, a karkashin jam’iyyar UPC, Adnan Mukhtar, ya bayyana dalilin da ya sa ya ke neman shiga majalisar tare kuma da hujjojin san a fita daga tafiyar Kwankwasiyya da ma jam’iyyar PDP gaba daya.
Mukhtar, wanda ke neman kujerar majalisar jiha, a matsayin wakilin karamar hukumar Nasarawa, ya ce ya fito ne domin kara karfafa dankon dimokradiyya tare da shuka ta a cikin zukatan matasa.
Mukhtar ya ce fitowa takarar a karkashin karamar jam’iyya ba ta kayar da masa da hankali, domin ya fito da tsarin wayar wa da matasa kai, ya na nuna musu cewa yanzu ne fa lokacin da ya kamata su farka daga barci.
Ya ce ya yi hirarraki da dama a gidajen radiyo, wadanda suka sa ya samu shiga a ruhin matasa masu tarin yawa.
” Na bi tafakin Kwankwasiyya a APC, kuma Kwankwaso ya san ni sosai. Lokacin da ya fice daga APC ya koma PDP, sai ni ma na bi shi muka koma PDP.
“Amma na raba hanya da kwankwaso, tun daga lokacin da batun takarar mukami a zaben fidda gwani ya taso. An kira taron sulhuntawa, inda Kwankwaso ya ce min wai na hakura da tsayawa takara, tunda ni yaro ne, ban dade da gama NYSC ba, kuma ba ni da aure.
“Kwankwaso ya ce min ba ni kuma da wani karfi a siyasa, don haka na kura da takarar kawai.
“Amma da na fahince kamar ‘yanci na ne ake so a tauye min, sai na koma wannan sabuwar jam’iyya, wato UPC.