Abin da ya sa mu ka hana APC tsaida ‘yan takara a Jihar Ribas – INEC

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana dalilan ta na hana APC tsaida ‘yan takara a jihar Ribas.

A cikin wata takarda da ta fitar jiya Juma’a a Fatakwal, babban birnin jihar, Kwamishinan Zabe na Tarayya, na Jihar Ribas, Obo Effanga, ya ce INEC ta bi umarnin kotu ne wadda ta haramta zabukan fidda-gwani da dangarorin da ke adawa na jam;iyyar suka gydanar, alhali akwai wata kara a gaban wata kotun da ta umarce su kada su kuskura su gudanar za zaben fidda-gwanin.

Ya ce APC bangaren Magnus Abe da ta bangaren Rotimi Amaechi, su na shari’a ne a gaban babbar kotun jihar dangane da rikitaccen zaben shugabannin jam’iyya da aka yi.

Magnus Abe ne ya kai kara cewa bangaren Amaechi ya gudanar da zabe, ba tare da saka bangaren sa a zaben ba.

A yanzu dai kotu da INEC sun cire sunan APC a zaben gwamna, na wakilan majalisar tsarayya da na sanatoci, har ma da majalisar dokoki ta jiha.

Share.

game da Author