Abin da ya sa ba zan mika kai na ga ’yan sanda ba – Dino Melaye

0

Sanata Dino Melaye, mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya fito ya yi magana daga inda ya ke boye, inda ya bayyana dalilan sa na kin mika kan sa ga ’yan sanda.

Melaye, wanda a baya ya ce idan ya kai kan sa ga ‘yan sanda, Sufeto Janar Idris Ibrahim zai iya yi masa allurar kisa domin ya kashe shi.

Melaye ya misalta abin da ya ke fuskanta da irin abin da ya ce Annabi Elijah ya fuskanta kamar yadda aka bada labari a cikin Bebul.

Ya fito ya yi bayanin haka jiya da yamma a cikin shafin sa na twitter, ya na mai kara cewa zai ci gaba da kasancewa a mabuyar sa.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda ‘yan sanda suka kewaye gidan Dino, a bisa tsammanin ya na cikin gidan, su na neman kama shi a bisa zargin hannun da ya ke da shi a fashi da makami da yunkurin kisa.

Wannan ne karo na hudu da ‘yan sanda suka yi tunkurin kama shi a cikin 2018.

Melaye ya bada labarin yadda Bebul ya bada labarin wani Annabi mai suna Elijah, wanda ya gudu ya boye a kan Tsaunin Carmel, bayan da Sarki Ahab na zamanin sa ya nemi kashe shi, saboda tsage gaskiyar da ya rika yi.

“Ni ba tsoron firowa na ke yi ba. Amma akwai bambanci tsakanin tsoro da kuma yin taka-tsantsan ko kuma yin kaffa-kaffa.” Haka ya fada a cikin shafin sa na twitter.

Melaye na neman a sake zaben sa sanata a karkashin jam’iyyar PDP.

Dama kuma ya na fuskantar tuhumomi na shari’a da ‘yan sanda suka gabatar da shi a kotuna biyu. Daya tuhumar a kan yunkurin sa na neman kashe kan sa da kan sa inji ‘yan sandan, sai kuma zargin bai wa ‘yan daba muggan makamai.

Amma kuma duk an bayar da belin sa a shari’un guda biyu.

Share.

game da Author