Babban Lauya Femi Falana, ya rubuta wa Hukumar Kare Hakkin dan Adam (NHRC), doguwar takarda, inda ya nemi gwamnatinn tarayya ta biya biyya ga iyalan masu gudun nhijira su 236 da sojojin sama suka jefa wa bam a Rann, jihar Barno, cikin 2017.
An dai jefa bam din ne a sansanin masu gudun hijira a bisa kuskure, tsammanin cewa sansanin Boko Haram ne.
Akalla masu gudun hijira 200 suka mutu a harin da aka kefa musu bam a ranar 17 GA Janairu, 2017.
Bayan kai harin, Babagana Malarima, wanda a lokacin Shugaban Karamar Hukumar Kala Balge, inda garin Rann ya ke, ya ce an kashe mutane 236.
Malarima ne ya sanar da wannan adadi bayan da hukumar tsaro ta sojoji da kuma gwamnatin tarayya sun yi kakarin boye adadin na wadanda aka kashe.
Tun a lokacin dama sai da Malarima ya shaida wa Babban Hafsan Askarawn Najaeriya, Tukur Buratai cewa, wadanda suka tsira da kuma iyalan wadanda aka kashe cewa suna neman a biya su diyya daga gwamnatin Najeriya.
Duk da dai cewa ba a bayyana ka’idojin yadda ake neman biyan diyyar ba, idan za a biya ne a bisa tsari na mulunci, to za a biya ran kowane mutun daya akan naira milyan 40.
Gaba daya gwamnatin tarayya za ta biya diyyar naira bilyan 9.5 kenan.
Shekaru biyu kenan bayan sojoji sun jefa bam din, amma har yanzu babu abin da gwamnatin tarayya ta yi.
Ganin cewa an cika shekaru biyu ba a yi komai ba, sai lauya Femi Falana ya dauki gaban gabarar neman musu hakkokin su.