9 – 0: PSG ta guma wa Guingamp guma-guman tsiya

0

Kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke Birnin Paris na kasar Faransa, ta sheka wa kungiyar Guingamp kwallaye tara a yau Asabar.

Fitaccen dan wasa Neymar Jr. ya ci kwallaye biyu haka shi ma Edson Cavani ya ci uku da Kylian Mpape si ma uku. Kowane ya yi ‘hatrick’ kenan.

An kusa tashi aka sako Thomas Meunier, wanda shi ne ya ci kwallo ta 9 din.

A yanzu PSG ce a kan gaba a gasar League na kasar Faransa, inda ta bai wa mai bi mata ratar maki 13.

Share.

game da Author