2019: ‘Yan shi’an bangaren El-Zakzaky sun halarci addu’ar bauta a Cocin St. Mary

0

‘Yan kungiyar Shi’a bangaren Sheikh Ibrahim El-Zakzaky sun halarci addu’ar bauta a Cocin St. Mary dake Sabon Gari, Zaria domin taya Kiristoci murnar shiga sabuwar shekara na miladiyya, 2019.

Isa Mshelgaru na sashen koyon gine-gine na jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ne ya jagoranci mambobin kungiyar zuwa wannan Coci a ranar Litinin.

” Mun zo wannan Coci ne domin mutaya abokanan zaman mu wato mabiya addinin kirista buki da addu’ar shiga sabuwar shekarar 2019. Mun yi haka ne domin mu kara dankon zumunci a tsakanin Musulmai da kiristocin da muke zaune tare a wannan karamar hukuma.

” Kashe-kashen juna da muke yi bai dace ba sannan bashi da wani asali a addinan mu. Allah daya ne ya halicce mu, dole ne mu zauna tare cikin kaunar juna da hakuri da juna.

Isah ya ce yin haka karantarwar shugaban su ne wato ibrahim El-Zakzaky.

A jawabin sa, shugaban Cocin Micheal Ibrahim Bazai ya jinjina wa wadannan mutane sannan ya yi addua’ar Allah ya ci gaba da hada kawunan mabiya addinan.

” Muna farin ciki da wannan ziyara da ‘Yan uwan mu mabiya addinin musulunci bisa wannan ziyara da suka kawo mana har wurin ibadar mu domin taya mu murnan shiga sabuwar shekara.

” Da gaske ne mukan ji tsoron zama kusa da juna saboda yadda kowa ke ganin idan har aka yi hakan ba za a wanye da dadi ba. Amma yanzu wannan ziyara da musulmai suka kawo mana nuni ne cewa duk ana tare kuma ana kaunar juna.

A karshe ya yi kira ga malamin jami’ar da a rika ba dalibai kiristoci guraben karatu a jami’ar ABU din sannan a rika saka su a kwasa-kwasai masu nagarta.

Share.

game da Author