2019: Mu da kan mu za mu kayar da APC a zaben gwamnan Ogun – Gwamna Amosun

0

Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, wanda dan jam’iyyar APC ne, ya kara shan alwashi da kuma bugun-kirjin cewa sai sun kayar da jam’iyyar ta su a zaben gwamnan jihar.

Amosun ya ce dan takarar da ya ke goyon baya, na jam’iyyar APM, Adekunle Akinlade ne zai lashe zaben.

Amosun ya kuma shawarci gwmnatin tarayya da kada ta tura sojoji a jihar a lokacin zabe, yayin da ya kara tabbatar da cewa za a gudanar da zabe mai inganci kuma sahihi a jihar Ogun.

Amosun ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke bayani a wurin taron murnar shiga sabuwar shekara a Oke-Ilewo, cikin Abeokuta, babban birnin jihar.

Gwamna Amosun wanda ya sake lashe zaben gwamnan jihar Ogun a karkashin APC a 2015, a yanzu ma ya fito takarar sanata ne a karkashin APC.

Sai dai kuma ba ya goyon bayan tan takarar gwamnan APC da ya yi zargin cewa su Bola Tinubu da Adams Oshimhole suka kakaba a jihar.

Amosun na goyon bayan dan takarar da ya nemi ya gaje shi, wato Akinlade, maimakon Dapo Abiodun na APC.

Akinlade ya fusata ya koma jam’iyyar APM da goyon bayan gwamna Amosun.

Share.

game da Author