2019: Kada ka maida Najeriya zamanin Tsarin Kasuwar Shinko – Gargadin Gwamnan CBN ga Atiku

0

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi fatali da tsarin da dan takarar shugabancinn kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai shigo da shi idan ya ci zabe, ya zama shugaban kasa.

Tun cikin 2016 ne CBN ta shigo da tsarin takura hada-hadar kudade da nufin inganta karfin darajar naira a kasuwar musayar kudaden kasashen waje da nufin karfafa kafadun tattalin arzikin Najeriya.

A karkashin wannan tsari, an kara sakin kudade, amma an takura tsarin hada-hadar ta hanyar tsaurara sa-ido inda aka samu kari daga kashi 12 bisa 100 a 2016 zuwa kashi 30 bisa 100 daga watanni masu yawa da suka shude zuwa yau.

CBN na bin tafarkin tsarin sakin kudaden ne wato ‘Liquidity’ bisa yin la’akari da karfin kudin ruwa na tsarin MPR da na CRR a Asusun CBN.
MPN tsurar kudin ruwan da CBN ke dora wa bankunan kasuwanci idan za su ramci a hannun babban bankin.

Shi kuma tsarin CRR shi ne yawan tsurar kudin da bankin kasuwanci ke ajiyewa na sa a babban bankin Najeriya.

Da ya ke hira a mujallar Afrika Report, Atiku ya ce idan ya zama shugaban Najeriya, zai sa CBN ya saki naira a kasuwar hada-hadar bankunan kasuwanci, domin ta fita ta nemar wa kan ta martaba da daraja inda za ta yi gogayya a kasuwa da kuma cikin kudaden musaya na kasashen duniya.

Wannan tsari na kasuwa-ci-mai-tsoron-ki da Atiku ya ce zai shigo da shi, shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefile ya ce ganganci ne.

“ Amma idan aka sake ta, ta tafi hada-hada a cikin cibiyoyin kasuwanci, ta haka ne tattalin arzikin kasa zai bunkasa, kuma masu zuba jari daga manyan kasashen duniya za su antayo domin kara gina masana’antun da za su habbaka tattalin arzikin mu.” Inji Atiku.

Shi kuma Emefile ya ce babu wani tsarin takure naira da CBN ke yi a yanzu, kuma CBN ba ya yin katsalandan wajen canjin kudi.

Amma ya ce ganganci ne tsarin da Atiku ya ce zai shigo da shi, wanda za a bar kowa ya rika shigo da abin da ya ga dama daga kasahen ketare da sunan habbaka tattalin arziki, ko kuma dadada wa wasu.

Ya ce wannan tsari an yi a baya, a lokacin gwamnatin Ibrahim Babangida, wanda aka kira SAP, wanda kuma bai zama mafita ba.

Share.

game da Author