2019: Jam’iyyun Siyasa (CUPP) sun ki amincewa da nada Amina Zakari babban mukami a zaben 2019

0

Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (CUPP) sun bayyana cewa bai wa Amina Zakari muhimmiyar rawar da za ta taka a zaben 2019 wani shiri ne domin a yi magudin zabe.

Jam’iyyun sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi, ta bakin kakakin su, Ikenga Ugochinyere.

Kungiyar ta nuna cewa nada ’yar uwar Buhari wato Amina Zakari a matsayin Shugabar Kwamitin Tattara Sakamakon Zaben Shugaban Kasa da INEC ta yi, shiri ne domin a yi magudi a zaben 2019.

CUPP sun ce nadin da aka yi wa Amina Zakari tsokanar rigima ce ko kuma shiri ne domin a yi wa ‘yan Najeriya karfa-karfa.

Sannan kuma kungiyoyin sun yi barazanar janyewa daga yarjejeniyar tabbatar da gudanar da zabe lami-lafiya da ‘yan takarar shugaban kasa na kowace jam’iyya suka sa wa hannu.

Sannan kuma sun ce shiri ne da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na ganin ko ta halin kaka ya sake cin zabe ko kuma ya sake komawa kan kujerar sa.

Sun ce idan aka yi la’akari da yadda Sufeto Janar ke yi wa ‘yan adawa hawan-kawara, da kuma nadin Amina Zakari, za a fahimci cewa magudi ne ko ta halin kaka ake kokarin yi domin kasancewa kan mulki ko ta halin kaka.

Share.

game da Author